Revelation of John 11

Shaidu Biyu

1Aka ba ni ƙara kamar sandan awo aka kuma ce mini, “Tafi ka auna haikalin Allah da bagaden, ka kuma ƙirga waɗanda suke sujada a can. 2Sai dai kada ka haɗa da harabar waje; kada ka auna ta, domin an ba da ita ga Alʼummai. Za su tattaka birni mai tsarki har watanni 42. 3Zan kuma ba wa shaiduna nan biyu iko, za su kuwa yi annabci na kwanaki 1, 260, saye da gwadon makoki.” 4Waɗannan su ne itatuwan zaitun biyu da kuma alkukai biyu da suke tsaye a gaban Ubangijin duniya. 5Duk wanda ya yi ƙoƙari yin musu lahani, wuta za ta fito daga bakunansu ta cinye abokan gābansu. Haka ne duk mai niyyar yin musu lahani zai mutu. 6Waɗannan mutane suna da iko su kulle sararin sama don kada a yi ruwan sama a lokacin da suke annabci; suna kuma da iko su juye ruwaye su zama jini su kuma bugi duniya da kowace irin annoba a duk lokacin da suke so.

7To, da suka gama shaidarsu, dabbar da takan fito daga Abis za ta kai musu hari, ta kuwa sha ƙarfinsu ta kuma kashe su. 8Gawawwakinsu za su kasance a kwance a titin babban birni, wanda a misalce ake kira Sodom da Masar, inda kuma aka gicciye Ubangijinsu. 9Kwana uku da rabi mutane daga kowace jamaʼa, kabila, harshe da kuma alʼumma za su yi ta ƙallon gawawwakinsu su kuma ƙi binne su. 10Mazaunan duniya za su ƙyaface su su kuma yi biki ta wurin aika kyautai wa juna, domin waɗannan annabawan nan biyu ne suka azabtar da mazaunan duniya.

11Amma bayan kwana uku da rabi ɗin numfashin rai daga Allah ya shige su, suka kuwa tashi tsaye, tsoro kuma ya kama waɗanda suka gan su. 12Sai suka ji wata babbar murya daga sama tana ce musu, “Ku hauro nan.” Suka kuwa haura zuwa sama cikin girgije, yayinda abokan gābansu suna ƙallo.

13A wannan saʼa aka yi wata babbar girgizar ƙasa kashi ɗaya bisa goma kuma na birnin ya rushe. Aka kashe mutane dubu bakwai a girgizar ƙasar, waɗanda suka tsira kuwa suka ji tsoro suka ɗaukaka Allah na sama.

14Kaito na biyu ya wuce; kaito na uku yana zuwa ba da daɗewa ba.

Ƙaho na Bakwai

15Malaʼika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji muryoyi masu ƙarfi a sama da suka ce:

“Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Kiristinsa,
zai kuwa yi mulki har abada abadin.”
16Sai dattawan nan ashirin da huɗu da suke zaune a kursiyoyinsu a gaban Allah, suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa suka kuma yi wa Allah sujada, 17suna cewa:

“Muna maka godiya ya Ubangiji Allah, Maɗaukaki,
wanda yake a yanzu, shi ne kuma a dā,
domin ka karɓi ikonka mai girma
ka kuma fara mulki.
18Alʼummai suka yi fushi; fushinka kuwa ya zo.
Lokaci ya yi don a shariʼanta matattu,
da kuma don sākawa wa bayinka annabawa
da tsarkakanka da kuma su waɗanda suke girmama sunanka,
ƙarami da babba— 
don kuma hallakar da waɗanda suka hallaka duniya.”
19Saʼan nan aka buɗe haikalin Allah da yake a sama, kuma a cikin haikalinsa aka ga sandukin alkawarinsa. Sai kuwa ga walƙiya, ƙararraki, tsawa, girgizar ƙasa, da kuma ƙanƙara masu girma.

Copyright information for HauSRK